IQNA

23:45 - February 05, 2019
Lambar Labari: 3483349
Bangaren kasa da kasa, za a buga tare da raba kwafin kur’anai dubu 120 a tsakanin wasu kasashen Afrika guda uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna, an cimma yarjejeniya tsakanin wasu madaba’antun kur’ani na Afrika da kuma kungiyar matasan musulmi ta duniya WAMY kan bugawa tare da raba kwafin kur’anai dubu 120 a tsakanin wasu kasashen Afrika.

Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar, inda za a fara gudanar da aikin nan ba da jimawa ba, domin tabbatar da cewa an raba wadannan kur’anai kafin nan da watan azumi.

Yarjeniniyar dai ta kunshi buga kwafin kur’anai  miliyan 4 wanda za a raba su a tsakanin kasashe dasuka hada har da na larabawa.

3787959

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، larabawa ، WAMY
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: