IQNA

22:29 - February 08, 2019
Lambar Labari: 3483357
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan ‘yan jarida sau 28 a cikin wata day a gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran UNA ya habarta cewa, a wata daya da ya gabata jami’an tsaron Isra’ila sun kaddamar da farmaki kan ‘yan jarida sau 28 a lokacin da suke gudanar da aikinsu na bayar da rahotanni.

Rahoton ya ce dukkanin ‘yan jaridar da aka kai wa hari an ci zarafinsu da kuma tozarta su ta hanayar lakada musu duka, da kuma kwace kayan aikinsu, yayin da 15 daga cikinsu an kame su, kuma ana tsareda su a gidan kaso, ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Irin wannan cin zarafi da jami’an tsaron Isra’ila suke yi wa ‘yan jarida da ma masu fafutuka daga kasashen ketare ba sabon lamari ba ne, babban abin mamaki shi ne yadda kasashen duniya suke yin gum da bakunansu kan irin wannan ta’asa da yahudawan suke aikatawa.

3788547

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، farmaki ، suke ، duniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: