IQNA

22:09 - February 20, 2019
Lambar Labari: 3483388
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da baje kolin hotunan juyin juya halin musulunci a Iran a kasar Afrika ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran qian, banagren sadarwa na cibiyar yada al’adun muslunci ya bayar da bayanin cewa, an gudanar da baje kolin hotunan juyin juya halin musulunci a Iran a kasar Afrika ta kudu.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan baje koli ya hada da hotuna na juyin juya hali da kuma rayuwar marigayi Imam Khomaini (RA) da gwagwarmayarsa domin ‘yantar da al’ummar Iran daga danniyar ‘yan mulkin mallaka.

Haka nan kuma an nuna hotuna ganawar tsohon jagoran kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela, musamman hotunan ganawarsa shugabannin kasar Iran da jami’an gwamnatin kasar,a  tsakanin shekarun 1992 zuwa 1999, a lokutan da ya ziyarci kasar ta Iran.

 

3791874

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: