IQNA

23:38 - February 22, 2019
Lambar Labari: 3483394
Bangaren siyasa, Na'ibin limamin masallacin jumma'a a nan Tehran, ya yi kira ga kasar Pakistan da kada ta zama sansanon horar da yan ta'adda masu cutar da kasashe makobta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Hujjatul Islam Mohammad Hassan Abuturabi Fard , na'ibin limamain masallacin jumma'a a nan birnin tehran yana fadar haka a cikin khudubobinsa na sallara jumma'a a yau.

Abuturabi fard ya kara da cewa, kasar Pakistan a matsayinta na kasar musulmi banda haka babbar makobciyar kasar Iran bai kamata ta zama tana tallafawa makiya JMI wajen cutar da ita ba. 

A ranar 13 ga watan Febrerun da muke ciki ne wasu yan ta'adda wadanda suka fito daga kasar Pakistan sula kai hari kan wata motar Bus dauke da dakarun juyin juya halin musulunci wadanda suka kammala aikinsu na tsaron kan iyakar kasa, suna komawa gida.

Sojojin 27 ne suka yi shahada sanadiyyar wannan harin a yayinda wasu 13 kuma suka ji rauni. Wata kungiyar yan ta'adda wacce ake kira "Dakarun Zalunci" ta dauki nauyin harin. .

A wani bangare na khudubarsa Hujjatul Islam Abuturabi fard ya bayyana cewa gwamnatin JMI zata ci gaba da riko da tsarin addinin musulunci a matsayin wanda zai gudanar da rayuwar mutanen kasar, kamar yadda ta riki shi shekaru 40 da suka gabata. 

3792290

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: