IQNA

23:51 - February 25, 2019
1
Lambar Labari: 3483402
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Isra’ila sun kame shugaban wakafin Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamafanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a yau jami’an tsaron yahudawan Isra’ila sun kame babban malami kuma shugaban wakafin falastinawa Sheikh Abdulazim Sahlab a gidansa  da ke birnin quds.

 

A nata bangaren gwamnatin kwarya-kwayan cin gishin kai ta falastinawa ta fitar da bayani na yin Allawadai da wannan mataki da Isra’ila ta dauka.

Bayanin ya ce kame wannan malami yana matsayin kame dukaknin al’ummar Palastine ne, kuma ya zama wajibi a gaggauta sakinsa ba tare da wani bata lokaci ba.

A cikin ‘yan kwanakin nan dai Isra’ila tana ci gaba da cin zarafin falastinawa a yankuna daban-daban na Palastine, musammana  yankunan gaza da kuma birnin Quds, wannan na zuwa ne tun bayan da falastinawa suka kudiri a niyar bude babu rahma wanda kuma ya gudana a ranar juma’a da ta gabata.

 

3792991

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، palastine ، gudana
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Saddik
0
0
Allah Saka Ma Palestinawa,Allah Ka Karya Yahudawa Ka Rusa Haramtacciyar Gwamnatinsu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: