IQNA

An Fara Gudanar Da Zaman Ministocin harkokin Wajen Kasashen Musulmi

19:46 - March 01, 2019
Lambar Labari: 3483414
Ministocin harkokin wajen kasashen musulmi sun fara gudanar da zamansu a yau a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, a yau Ministocin harkokin wajen kasashen musulmi sun fara gudanar da zamansu a yau karo an 46 a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Ministan harkokin wajen kasar hadaddiyar larabawa Abdullah Bin Zaid Ali nahyan shi ne ya bude taron da jawabinsa, inda ya bayyana cewa za tattauna muhimman batutuwa da suke ci ma muuslmi tuwo a kwarya, musamman batun ayyukan ta’addanci.

Haka nan kuma ya bayyana batun Palastine ad cewa shi ne batu na farko ga duniyar musulmi wanda ba za a taba mantawa da shi ba, inda dukkanin musulmi suke fatan ganin an kafa kasar palastine mai cin gishin kanta a kan iyakokinta na shekara ta 1967.

Dangane da batun tsaro kuwa, ya ce dole ne kasashen musulmi su mike domin hana yaduwar tsatsauran ra’ayi wanda yake haifar da ta’addanci.

3794318

 

 

 

 

 

 

captcha