Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Mukhtar Juma’a minister mai kula da harkokin addini a kasar Masar ya ce za a rika tarjama hudubar juma’a zuwa harzuna 17 a nan gaba.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu daliban addini na kasar wadanda ake turawa domin jagorantar cibiyoyin addini da masallatai bayan sun kammala karatu.
Y ace ko shakka babu hudubobin juma’a akwai abubuwan da suke koyar da dan adam na kyawawan halayae da tunatarwa gare shi, wanda hatta wadanda ba muuslmi suna da bukatar su san me ake cewa.