IQNA

Paparoma Zai Kai Ziyara A Kasar Musulmi Karo Na Biyu

23:56 - March 28, 2019
Lambar Labari: 3483502
Bangaren kasa da kasa, Paparoma Francis zai kai ziyara a kasar Morocco domin gudanar da tattaunawa Kan lamurra na addini da kuma hijira.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, a ranar Asabar shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darikar Katolika Paparoma Francis zai ziyarci kasar Morocco

Kimanin mutane 30,000 ne mabiya adinin kirista za su taru domin i tarbarsa, akasarinsu dai ‘yan kasashen Afrika ne da suke karatua  kasar ta Morocco.

Haka nan kuma zai jagoranci wani taron addinin a babban filin wasanni na birnin Rabat, tare da halartar mabiya addinin kiista kimanin dubu 10.

Wannan dais hi ne karo farko da wani jagoran kiristoci na duniya zai ziyarco Morocco tun daga shekara ta 1985, a lokacin paparoma John Pol ya ziyarci kasar.

Sarki Hassan na biyu shi ne wani shugaban larabawa da ya gayyaci paparoma zuwa kasarsa, kuma a shekara ta 1991 shi ma ya ziyarci fadar Vatican.

 

3800132

 

captcha