IQNA

23:01 - April 08, 2019
Lambar Labari: 3483532
Rahotanni daga kasar Libya na cewa, akalla mutane 2200 ne suke fice daga birnin Tripoli fadar mulkin kasar, domin tsira da rayukansu daga rikicin da ya kunno kai a birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, ya zuwa mutane kimanin 2200 suka fice daga birnin Tripoli, sakamakon artabun da ake yi tsakanin dakarun da ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasar, da kuma sojojin da suke biyayya ga janar Khalifa Haftar.

Hukumar agajin gaggawa ta majalisar dinkin duniya ta bayar da rahotanni da suke bayyana halin da wadannan mutane suke ciki, inda da dama daga cikinsu ba su da isassun kayayykin bukatar rayuwa tare da su, domin kuwa sun fice ne a cikin firgici da tsoro.

Rahoton na hukumar ya ce yanzu haka akwai dubban mutane da aka killace su a kudancin birnin Tripoli, kuma ba za su iya fita daga yankunan nasu ba, domin tsoron abin da ka iya samun rayuwarsu.

A nasa bangaren mataimakin Firayi ministan kasar ta Libya Ali Alkatrani ya sanar da yin murabus dinsa, bayan da dakarun Haftar suka killace birnin Tripoli ta bangarori daban-daban, yayin da shi kuma firayi ministan kasar Faiz Siraj ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kare birnin Tripoli da dukkanin karfinsu.

3801946

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Libya ، tripoli ، Haftar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: