Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, mataimakin ministan tsaron kasar Sri Lanka Ruwan Wijewardene ya fadi a jiya cewa, hare-haren da aka kai a kasar a kan majami’oi da otel-otel an kai su domin daukar fansa kan harin da aka kai a kan masallatai a garin Christ Church na kasar New Zealand.
Mataimakin ministan tsaron kasar ta Sri Lanka ya ce; sakamakon bincike na farko-farko yana nuni da cewa, wadanda suka shirya kai harin sun yi hakan ne da suna daukar fansa kan harin New Zealand, kuma ana zargin kungiyar ‘yan salafiyya masu tsatsauran ra’ayi da ake kira Jama’at Milli Tauhid da hannu a harin.
To sai dai wasu bayanai daga bangaren jami’an tsaron kasar na cewa, mai yiwuwa akawai hannun ‘yan ta’addan kungiyar Daesh a hare-haren, amma ba a riga an tabbatar da hakan ba kawo ya zuwa yanzu.
A jiya Talata jami’an tsaro masu bincike sun kame wani mutum dan akasar Syria, wanda ake zargin cewa yana da hannu a harin, bayan kame wasu mutane kimanin 40 dukkaninsu ‘yan kasar ta Sri Lanka ne, wadanda ake zargin suna da alaka da hare-haren.