IQNA

23:53 - April 30, 2019
Lambar Labari: 3483590
Bangaren kasa da kasa, wata tawagar kwamitin kare hakkokin musulmi na Islamic Human Rights Commission IHRC, da ke kasar Birtaniya ta  isa Najeriya, domin duba lafiyar Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi kusan shekaru 4.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tawagar wadda ta kunshi kwararrun likitoci karkashin jagorancin babban sakataren kwamitin Mas'ud Shajareh, ta isa Najeriya ne bayan samun izini daga mahukuntan kasar, inda suka gana da Sheikh zakzaky tare da duba lafiyarsa.

Babban sakataren kwamitin na IHRC Mas'ud Shajareh ya bayyana cewa, babbar manufar ziyarar ta su a Najeriya ita ce duba halin da Sheikh zakzaky yake ciki kan batun rashin lafiyarsa, domin sanin irin kulawar da yake bukata dangane da lafiyar tasa.

Ya ce yanayin da malamin yake ciki yana bukatar kula ta musamman, idan aka yi la'akari da cewa akwai matsalolin da yake fama da su da suke da bukatar kulawar likitoci ta musamman, da hakan ya hada da hawan jini, da kuma matsalar idanunsa, inda  a halin yanzu daya daga cikin idanunsa ba ya aiki, dayan kuma na bukatar dubawa domin ganinsa ya fara rauni, baya ga raunukan da ya samu sakamakon harbi da harsasan bindiga a lokacin da aka kama shi.

Shajareh ya ce dukkanin wadannan abubuwa ne da suke bukatar kulawa ta musamman daga liktoci na musamman, da kuma kayan aiki na musamman, bisa la'akari da hakan, wannan yasa suke ganin ya kamata a kula da Sheikh Zakzaky ne a wajen Najeriya, a wasu asibitoci na kasashen ketare da ke da isassun kayan aiki na zamani domin ceton lafiyarsa.

A nata bangaren gwamnatin kasar Iran ta yi na'am da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka, na barin kwararrun likitoci na kwamitin IHRC daga London su duba Sheikh Zakzaky, domin sanin yanayin lafiyarsa.

Tawagar kwararrun likitocin na kwamitin IHRC sun tattara bayanai dangane da binciken da suka yi kan yanayin lafiyar Sheikh Zakzaky, inda daga karshe dai suka kai ga matsaya kan cewa akwai bukatar a fita da shi zuwa asibitocin kasashen wajen, wanda kuma hakan yana bukatar amincewa daga bangaren mahukuntan tarayyar Najeriya.

Bayan mika sakamako na karashe kan binciken, mahukuntan Najeriya ne ke da hakkin yanke matsaya ta karshe kan amincewa ko rashin hakan, dangane da bukatar fitar da malamin daga Najeriya zuwa kasashen waje, domin kula da lafiyarsa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ba ta ce komai ba a hukumance  dangane da wannan batu, amma kwamitin na IHRC tare da wasu bangarori na daban, suna ci gaba da bin kadun batun ta hanyoyin da suka dace, domin ganin an samu amincewa daga bangarorin da abin ya shafa, ta yadda hakan zai bayar da damar fitar da malamin zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa. 

3806996

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، lafiyarsa ، bukatar ، zakzaky
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: