IQNA

23:58 - May 08, 2019
Lambar Labari: 3483619
Ofishin firayi ministan kasar Iraki ya fitar da bayani kan zyarar da sakatarn harkokin wajen Amurka ya kai a daren jiya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillacin Samaria News ya bayar da rahoton cewa, a yau Ofishin firayi ministan kasar Iraki ya fitar da bayani kan zyarar da sakatarn harkokin wajen Amurka ya kai a daren jiya a kasar da kuma abin da ziyarar ta kunsa.

A yayin ziyarar firayi ministan Iraki Adel Abdulmahdi ya jaddada muhimmanci alaka tsakanin Iraki da Amurka, inda ya ce irin siyasa da kasarsa ta dauka ita ce mafi dacewa, inda take hullda da dukkanin kasashen duniya.

Ya kara da cewa kasarsa tana yin mu’amala da dukkanin kasashen yankin gabas ta tsakiya da dukkanin makwaftanta ba tare da shiga cikin matsalolin kasashe ba.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa; Iraki na da matukar muhimmanci ga Amurka, a kan suna bukatar Iraki ta ci gaba da bin wannan salon siyasa, kuma suna bukatar ta baiwa Amurkawa da ke kasar kariya daga duk wata barazana.

 

3810073

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، pompeo ، Amurka ، Iraki ، Iran
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: