IQNA

23:57 - May 11, 2019
Lambar Labari: 3483630
Dubban mutane sun gudanar da jerin gwanoa birane daban-daban na kasar Birtaniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin Palastine online ya bayar da rahoton cewa, mutane sun gudanar da jerin gwanoa birane daban-daban na kasar Birtaniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastine da suke fuskantar zalunci da danniya.

An gudanar da wannan jerin gwano a gaban ginin BBC da ke Landan da ma wasu birane da dama na kasar Birtaniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da yahudawan sahyuniya suke shirin gudanar da tarukansu na Nakba, wato tunawa da lokacin da suka mamaye Palastine.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da masu fafutukar kare demukradiyya da kungiyoyin lauyoyi da na farar hula daban-daban ne suka shirya wannan jerin gwano a fadin kasar ta Birtaniya, domin nuna rashin amincewa da irin zaluncin da al'ummar Palastine ke fusknata daga yahudawan sahyuniya.

3810674

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: