IQNA

23:52 - May 14, 2019
Lambar Labari: 3483638
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran ya ce babu batun tattaunawa da Amurka, yin tsayin daka da jajircewa a gaban Amurka shi ne zai sanya ta sake tunani.

Kamfanin dillancin labaran iqna,

Jagoran ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake ganawa da jami’an gwamnatin kasar ta Iran a birnin Tehran, inda ya ce tattaunawa da Amurka musamman gwamnatin da ke kan mulki yanzu, na a mtsayin guba ne, kuma babu batun yakin da suke ta babatu a kansa.

Jagoran ya ce; babban abin da Amurka take son ta tattauna da Iran a kansa shi ne karfin da Iran take das hi, da kuma yadda za a raunana wannan karfi, wanda kuma babu wani ba’iraniye mai hankali da zai taba amincewa da hakan.

Ya ce abin da ke gaban Iran da al’ummarta shi ne ci gaba da jajircewa a kan matsayinsu na kin mika wuya ga manufofin mulkin mallaka, tare da ci gaba da dogaro da Allah da kuma kara bayar da himma wajen ci gaban kasarsu ta hanyar dogaro da kansu ta hanyoyin bunkasa ilimi da kere-kere.

Jagoran ya ce;  babban manufar Amurka ita ce mayar da Iran ta zama ‘yar amshin shata, wanda kuma kasa mai ‘yancin siyasa da sanin ciwon kanta, da kishin addininta da al’ummarta, ba za ta taba zama ‘yar amshin shata ga wata kasa ba.

Ya kara da cewa, dukkanin matakan kiyayya da gaba da Amurka take dauka a kan kasar Iran tsawon sama da shekaru arba’in, su ne suka kara taimaka ma kasar wajen dogaro da kanta, da kuma samun ‘yancin siyasa.

 

 

3811631

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: