IQNA

23:52 - May 17, 2019
Lambar Labari: 3483648
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar New Zealand ba su amince ad shirya wani fim da zai nuna yadda aka kai hari kan masallacinsu ba.

Kamfanin dilancin labaran iqna, shafin yada labarai na cibiyar cibiyar musulmin ankin Couter Berry a kasar New Zealand ya bayar da rahotoon cewa, babbar cibiyar musulmi ta yakin MAC ba ta amince da yunkurin shirya fim kan abin da ya faru na kai hari kan muuslmi a garin Christ Church ba.

Muiz Mas'ud wani mai shirya fina-finai nea  kasar Masar,a  makon da ya gabata ya sanar da cewa, suna da niyyar shirya wani fim kan hakikanin abin da ya faru ga musulmi a New zealand lokacin da aka kai musu har a masallaci.

Cibiyar muuslmin ta New Zealand ta ce, shirya wannan fim ba maslaha ce gare su ba, kamar yadda kuma ba maslaha ce ta al'ummar musulmi ba, domin kuwa yin hakan zai tunzura wasu daga cikin musulmi su aiwatar da wani aiki makamancin hakan a kan wadanda ba musulmi ba da sunan daukar fansa.

3812118

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: