IQNA

A jiya ne aka gudanar da jirin gwanon ranar Quds ta duniya a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, wanda ya samu halartar dubban musulmi.

A kowace shekara ana gudanar da jerin gwano da taruka na ranar Quds ta duniya a kasashe daban-daban, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastine, akmar yadda marigayi Imam Khomaini (RA) ya ayyana wannan rana a matsayin ranar Quds ta duniya.