Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Jad Muhamamd Alkadi shugaban babbar cibiyar kula da ayyukan ilimin taurari ta kasar Masar ya fadi cewa, bisa lissafin ilimin taurari da kuma la’akari da juyawar lokutan tsayuwar wata, a yammacin yau Litinin bayan faduwar rana, a wasu daga cikin kasar ta Masar za a ga jinjirin wata tsawon mintuna 5 zuwa 7.
Ya ce duk kuwa da cewa akwai babbar cibiyar addini ta Darul fatawa da ke yanke hukunci na karshe a hukuamnce, amma dai a ilmance wannn sakamakon bincikensu.
Akwai cibiyoyi kimanin 10 da suke karkashin cibiyar fatawa ta kasar masar ad suke gudanar da ayyukan dubar wata a kasar, wadanda sukan yi hadin gwiwa da babbar cibiyar kula da ayyukan ilimin taurari ta kasar.