IQNA

23:52 - June 03, 2019
Lambar Labari: 3483706
'Yan siyasa da kungiyoyin gwagwarmaya na kasashen Larabawa sun gudanar da taron kin amincewa da yarjejjeniyar Karni a Beirut.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habatar cewa a wannan lahadi, 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula gami da kungiyoyin gwagwarmaya na kasashen Larabawa sun gudanar da taron kalubalantar taron yarjejjeniyar karni da aka shirya gudanarwa a Manamah, a birnin Bairout na kasar Labnon.

Taron na Manamah fadar milkin kasar Bahren da aka shirya gudanarwa cikin ranaukun 25 da 26 na wannan watan yuni da muke ciki, na a matsayin matakin farko na zartar da yarjejjeniyar karni da kasar Amurka gami da haramtacciyar kasar Isra'ila ke son aiwatarwa a yankin.

Mahalarta taron na Bairout sun tabbatar da cewa kasashen musulmi za su wargaza wannan yarjejjeniya ta karni, sannan sun bukaci kasashe da su dauki matsaya guda na hana wannan shiri na Amurka.

Ziyad Al-Nakhaleh babban saktare kungiyar gwagwarmayar musulinci ta Palastinu ya ce goyon bayan da Amurka ke bawa Isra'ila ido rufe shi ne dalilin da ya sanya take fice gona da iri kan al'ummar Palastinu, domin haka kungiyar gwagwarmayar musulinci za ta ci gaba da gwagwarmaya da take yi kuma babu batun ja da baya har abada.

Bisa tsarin da Amurka ta gabatar na yarjejjeniyar karni shi ne Qudus mai tsarki zai kasance babbar Hedkwatar Isra'ila, sannan Palastinawan dake gudun hijra a kasashen ketare ba su da 'yan ci dawo wa Palastinu.

 

3816707

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: