IQNA

23:51 - June 07, 2019
Lambar Labari: 3483717
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta kori kasar Sudan daga kungiyar har zuwa lokacinda za’a dawo tsarin democradiyya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayyana cewa Kungiyar ta dauki wannan matakin ne a wani taron gaggawa wanda komitin tsaro da sulhu na kungiyar ta kira a jiya Alhamis.

Har’ila yau kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan dirar mikiyan da sojojin kasar Sudan suka yiwa fararen hula masu zaman dirshen a gaban ginin ma’aikatar harkokin tsaron kasar a ranar litinin da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dari.

Masu zaman dirshen suna bukatar sojojin su mika mulki ga fararen hula, bayan da tattaunawa tsakanin sojoji masu mulkin kasar da kuma kungiyoyin fararen hula daban daban na kasar ya wargaje a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Banda haka kungiyar ta Au ta tura Firai Ministan kasar Ethiopia Abiy Ahmed a matsayin mai shiga tsakanin sojojin da kuma kungiyoyin fararen hula na kasar ta Sudan. Ana saran Fri Ministan zai Isa birnin Khartun babban birnin kasar ta Sudan a yau Jumma’a.

Tuni dai kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da matakan da kungiyar Au ta dauka. Sannan gwamnatin kasar Britania ta kira jakadan Sudan a London don nuna masa bacin ran gwamnatin kasar kan kisan da sojojin suka yi a ranar litinin da ta gabata.

 

3817467

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: