IQNA

23:59 - June 09, 2019
Lambar Labari: 3483723
An fara gudanar da bore da yajin aiki a fadin kasar Sudan da nufin tilasta ma sojojin kasar mika mulki ga hannun fara hula.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, Jam’iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula a Sudan sun kirayi magoya bayansu da ma al’ummar kasar baki daya, da su fara bore na kasa baki daya.

Wannan kira ya zo ne bayan kame wasu daga cikin manyan jagororin ‘yan adawar siyasar biyu da sojoji suka yi a jiya, biyo bayan ganawar da suka yi da firayi ministan kasar Habasha, wanda ya ziyarci Sudan a ranar Juma’a da ta gabata, domin sasanta bangarorin rikicin kasar.

Jam’iyyun siyasar da kungiyoyin farar hula sun bukaci a jama’a da su rufe hanyoyi a manyan birane, tare da kaurace wa wuraren ayyuka, domin tabbatar da cewa komai ya tsaya cak a kasar, ta yadda sojoji ba za su iya aiwatar da komai ba.

Jam’iyyun siyasar sun ce sun dauki wanna matakin ne bayan da majalisar sojojin kasar ta dauki matakin yin fito na fito da al’ummar kasar.

 

3817812

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sudan ، jerin gwano
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: