IQNA

23:39 - June 18, 2019
Lambar Labari: 3483749
Bangaren siyasa, Hojjatol Islam Rauhani shugaban kasar Iran, ya bayyan acewa kasar za ta yi nasara a kan makiya masu shirya mata makirci a fadin duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran dakta hasan Rouhani ya ce tushen yakin da masu bakar aniya suka shiga da al'ummar Iran, shiryeyyen yaki ne sannan ya tabbatar da cewa jajircewar da kuma fatan da Al'ummar Iran suke da shi, zai sanya su hana makiya cimma manufofinsu.

A yayin da ya halarci bikin buda bangaren kwasar fasinja na Salam a filin sauka da tashin na jiragen saman kasa da kasa na Imam Khomeini International Airport a wannan talata, Shugaban jamhoriyar musulinci ta iran dakta Hasan Rouhani ya ce duk da matsin lambar tattalin arziki da makiya ke yiwa Al'ummar Iran na yanke kauna, to amma ko wata Rana, al'ummar kasar na kirkiro wasu sabin abubuwa na ci gaban kasar

A yayin da yake ishara kan rashin cin nasarar Amurka na yanke duk wata alaka tsakanin Iran da kasashen Duniya, Shugaba Rouhani ya ce duk irin kokarin da hukumomin kasar Amurka ke yi a yayin tarukan kasa da kasa da ake yi na bata suran Iran, har yau har gobe kasar Iran nada kyakkyauwar alaka da sauran kasashen Duniya.

Shugaban kasar Iran ya tabbatar da cewa martani da kasashen Duniya ke mayar wa Amurka na jinjinawa kasar Iran shi kadai ya isa kunya ga hukumomin Amurkan, domin a yau mafi yawan kasashen Duniya na jinjinawa kasar Iran kan riko da alkawarin kasa da kasa da ta yi, yayin da suke kallon Amurkan a matsayin kasa maras alkawari da take aiki da dokokin da suka sabawa adamtaka.

A wannan Talata ce aka bude wani katafaran wurin daukan fasinja da zai iya daukan matafiya sama da dubu 5 a filin sauka da tashin na jiragen saman kasa da kasa na Imam Khomeini International Airport, wanda injinoyiyn kasar Iran suka gina ba tare da hadin gwiwar kasashen waje ba.

3820327

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: