IQNA

23:00 - June 20, 2019
Lambar Labari: 3483756
Rundunar kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta yi karin haske kan batun harbo jirgin Amurka maras matuki na leken asiri.

Hukumar gidan radio da talabijin ta kasar Iran ta nakalto Rundunar kare juyin juya halin musulinci na kasar Iran cikin wani bayani da ta fitar ta ce jirgin Amurka maras matuki na leken asiri samfurin Global Hawk ya tashi a karfe 12  da mintuna  14 na daren jiya laraba daga sansanin sojin kasar Amurka na kudancin tekun Fasha, inda ya fara shawagi a sararin samaniyar yankin tekun fasha, daga karshe ya nufi yankin Chabahar dake kudu maso gabashin Iran da nufin leken asiri.

Sanarwar ta kara da cewa yayin da jirgin Amurka maras matuki ke cikin tattara bayanai sirri a kan hanyar dawowarsa daga yankin na Chabahar a daidai yankin Hormozgan da misalin karfe hudu da minti biyar na safiyar wannan Alhamis dakarun tsaron juyin juya halin musuluncin kasar suka harbo shi.

Wannan jirgin na Amurka maras matuki samfurin Global Hawk ko kuma RQ4C na daga cikin mahiman jiragen yakin Amurka na leken asiri da kasar ke takama da shi, inda bayanai ke cewa kimarsa ta kai milliyan 200 na dalar Amurka.

3820994

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iran ، jirgin ، yaki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: