IQNA

23:43 - June 23, 2019
Lambar Labari: 3483764
Bangaren kasa da kasa, an mayar da dadadden kwafin kur’ani da aka tarjama zuwa babban dakin ajiye kayan tarihi na birnin Wellington a New Zealand.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya aka dauke dadden kwafin kur’anin nan da aka tarjama tsawon daruruwan shekaru a cikin ahrshen turancin Ingilishi zuwa babban dakin ajiye kayan tarihi an New Zealand.

A anann wuri akwai tsoffin litatfai kimanin guda 200 da ake ajiye su a wurin, inda a halin yanzu aka hada su da wani kwafin kur’ani da aka tarjama da jimawa.

Wani marubuci mai suna George Sale dan kasar Ingila ne ya yi wannan tarjama a shekara ta 1734 da ya kira (kur’anin Muhammad).

Wannan tarjama ta kunshi shafuka 470, kamar yadda kuma yak an yi sharhi a kasan kowane shafi.

 

 

 

3821613

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: