IQNA

23:46 - June 23, 2019
Lambar Labari: 3483765
Al'ummar Bahren sun yi Allah wadai da taron kin jinin al'ummar Palastinu da ake shirin gudanarwa a Manama fadar milkin kasar Bahrain

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a daren jiya assabar al'ummar birnin Manama sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da taron da ake shirin gudanarwa a birnin, inda suka bayyana fishinsu a fili kan matakin da gwamnatin Ali khalifa da wasu kasashen Larabawa suka dauka na kasancewa tare da Amurka gami da haramtacciyar kasar Isra'ila wajen tauye hakkin al'ummar Palastinu da batun Qudus mai tsarki.

Kafin hakan dai, kungiyoyi da masu rajin kare hakkin bil-adama na kasar sun nuna adawarsu da gudanar da Taron Amurka-Sahayuna a birnin na Manama.

A ranaikun 25 da 26 ne ake sa ran za a gudanar da taron tattalin arziki a kasar Bahren dake a matsayin matakin farko na gudanar da shirin yarjejeniyar karni.

Ita dai yarjejeniyar Karni, shiri ne da kasar Amurka ta gabatar wanda zai shafe duk wasu hakkoki na al'ummar Palastinu, sannan kuma birnin Qudus ya zamanto fadar milkin haramtacciyar kasar Isra'ila, Palastinawa dake gudun hijra a kasashen ketare ba su da hakin koma kasarsu ta haifuwa,kuma abinda zai ragewa Palastinu shi ne yankunan dake gefen kogin Jodan da yankin zirin Gaza.

3821580

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: