IQNA

23:59 - June 24, 2019
Lambar Labari: 3483768
Bangaren kasa da kasa, kungiyar malai ta duniya ta yi watsi da shirin yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babbar kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wani bayani da ke bayyana taron da ake shirin gudanarwa a Bahrain kan Palastine da cewa cin amanar musulmi ne.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ta fitar, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kakkausar suka kan taron da ake shirin gudanarwa a birnin Manama na kasar Bahrain kan Palastine, inda ta ce taron cin amanar musulunci da ma dukkanin ‘yan adam ne.

Bayanin ya kara da cewa, abin ban takaici ne yadda wasu daga cikin sarakunan kasashen larabawa suka zama ‘yan koren Amurka da yahudawa, ta yadda suka zabi su sayar da addininsu da al’ummarsu domin biyan bukatun Amurka da yahudawa.

A kan haka kungiyar ta ce tana kiran musulmi da sauran kasashe masu ‘yancin siyasa da su nisanta kansu daga wannan taro na cin amana, wanda Amurka da Isra’ila gami da Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suka shirya domin sayar da Palastine.

3821799

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: