IQNA

Babu wata kasa wadda take son su, amam dole ne a kare su. Wasu rahottani na cewa 'yan Rohingya suna iya komawa kasarsu ta Myanmar don kashin kansu idan suna bukatar hakan. Amma wasu jami'ai na UN suna cewa, mai yiwuwa 'yan kabilar Rohingya za su ci gaba da zama a inda suke a halin yanzu har zuwa wasu shekaru masu zuwa, inda za a mayar da wannan sansani nasua matsayin sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya. Tun a cikin 2017 ne sojojin Myanmar suka yi ma musulmin Rohingya kisan kiyashi, lamarin da yasa suka bar kasarsu.