Kamfanin dillancin labaran iqna,
A cikin bayanin da ta fitar, Harkar musulunci ta bayyana cewa a sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka gudanar bayan dibar jinin sheikh Zakzaky, an gano cewa akwai sanadaran lead, da candimum a cikin jininsa mai tarin yawa.
Bayanin ya ce likitocin sun tabbatar da cewa irin wanna yanayi yana da matukar hadari, kuma idan ba a gaggauta daukar mataki na tunkarar lamarin ba, to rayuwarsa tana cikin hatsari.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata ne dai wata tawagar likitoci daga kwamitin kare hakkokin musulmi na kasar Birtaniya suka ziyarci Sheikh zakzaky, sun kuma bukaci da a bayar da damar fitar da shi domin yi masa magani.
Magoya bayan Harkar Muslucni a Najeriya suna gudanar da jerin gwano da gangamiabirnin Abuja da wasu biranan kasar, domin yin kira ga mahukunta domin su saki Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa domin duba lafiyarsu.