IQNA

22:58 - June 30, 2019
Lambar Labari: 3483795
Bangaren kasa da kasa, sojojin kasar Sudan sun kai hari kan wuraren da 'yan adawa suke taruwa a cikin babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin aljazeeranet ya bayar da rahoton cewa,

a jiya Asabar  jami'an tsaron Sudan sun kai farmaki kan babban ofishin gamayyar kungiyoyin adawa na ' neman 'yanci da sauyi tare da hana 'yan adawa gudanar da taron manema labarai

A wannan lahadi ma 'yan adawar sun kira gagarumar zanga-zanga ta nuna adawa da kama karyar da Majalisar Soja dake rike da madafun ikon kasar Sudan din ke yi,

A halin da ake ciki bangaren 'yan adawar na Sudan na zargin sojin kasar da zubar da jinin al'ummar kasar, inda su ma sojojin ke dora alhakin abinda ya faru a baya kan shugabanin gamayar kungiyar neman sauyi da 'yanci na kasar.

A ranar 11 ga watan Afirilu da ya gabata ne Sojin kasar Sudan din suka kifar da gwamnatin Albashir, tare kuma da kafa Majalisar Soja wacce za ta ci gaba da jan ragamar mulkin kasar, to saidai al'ummar Sudan din sun ci gaba da zanga-zanga na neman mika mulki ga farar hula

An gudanar da tattaunawa da dama kan yadda za a kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin Sojoji da fararen hula ba tare da cimma matsaya ba, matakin amfani da karfi da Majalisar Sojin kasar ta dauka na tarwatsa masu zaman dirshin da zanga-zanga wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 130 ya yi sanadiyar dakatar da tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

 

3823120

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: