IQNA

23:55 - July 09, 2019
Lambar Labari: 3483823
Jami’an tsaron Isra’ila sun kame falastinwa 25 a yammacin jiya a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ajiya jami’an tsaron yahudawan Isra’ila dauke da muggan makamai sun kutsa kaia a cikin yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordaninda suka yi awon gaba da wasu matasa falastinawa 25.

Shedun gani da ido sun ce, jami’an tsaron yahudawan sun kame matasan ne ba tare da wani dalili ba, kuma sun tafi da su wani wuri da ba a sani ba, kamar yadda kuma iyayaen matasan ba su san makomarsu ba.

A cikin ‘yan lokatann nan jami’an tsaron yahudawan suna tsanananta matakai a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan, bisa abin suke kira barazanar tsaro da matsugunnan yahudawa da ke cikin wadannan yankuna suke fuskanta daga falastinawa.

Yanzu haka dai akwai falastinawa kimanin dubu biyar da dari bakwaicikin gidajen kurkukun Isra’ila, da suka hada da mata da kananan yara, da kuma ‘yan jarida gami da likitoci.

 

3825493

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: