IQNA

23:49 - July 10, 2019
Lambar Labari: 3483826
Bangaren kasa da kasa, wani mutum da ba a san ko wane ne bay a keta alkur’ani mai tsarki a wani masallaci a Kuwait.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na tashar Iram News ya bayar da rahoton cewa, a jiya wani mutum da ba a san ko wane ne bay a keta alkur’ani mai tsarki a wani masallaci a Kuwait a yankin Alqusur.

Bayan faruwar lamarin wani mutum wanda ya fara ganin abin da ya faru ya gaggauta sheda wa yan sanda, nan da nan kuma suka shiga gudanar da bincike domin gano masu hannua  cikin wannan lamarin.

Wannan dai bas hi ne karon farko da ake samun irin wannan ba a kasar Kuwait, domin kuwa a cikin shekara ta 2013 ma an samu wasu mutane da suka keta kur’ani mai tsarkia  cikin wasu masallatai, yayin da kuma wasu suka kona kur’ani.

 

 

3825701

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: