IQNA

23:51 - July 12, 2019
Lambar Labari: 3483832
Bangare kasa da kasa, sojojin da ke mulki a Sudan sun sanar da dakile wani yunkirin juyin mulki a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kwamitin tsaro a Majalisar mulkin sojojii ta rikon kwarya a Sudan ya bada sanarwan cewa Mahukuntan kasar sun yi nasarar rusa wani sabon yunkurin juyin mulki a kasar.

A bayanin da kwamitin tsaron ya fitar ta hanyar tashar talabijin ta kasa a yammacin jiya Alhamis ya ce gwamnatin ta sami nasarar rusa wani yunkurin juyin mulki a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan, amma bai bayyanan wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin ba.

Labarin ya kara da cewa Tuni an kame wasu gungun sojoji da suke da hannu a shirya yunkurin juyin mulkin, da nufin janyo cikas a kokarin da ake yi na cimma yarjejeniyar siyasa tsakanin rundunar sojojin kasar da kungiyoyin da jam’iyyun siyasa masu rajin ‘yanci da wanzar da canji a kasar.

 

3826403

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sudan ، sojoji
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: