IQNA

23:57 - July 28, 2019
Lambar Labari: 3483891
Bangaren siyasa, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya dora alhakin tashe-tashen hankula da suke faruwa a gabas ta tsakiya a kan sijojin kasashen ketare da ke yankin.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran ya bayyana cewa kasancewar dakarun tsaron kasashen waje a yankin ba wai kawai baitaimaka wajen tabbatar da tsaro ba , saidai ne shine tushen tayar da hargitsi a yankin.

Yayin da yake ganawa da Yusuf bn Alawi ministan harakokin wajen Oman a nan birnin Tehran Shugaban kasar Iran Dakta hasan Rouhani ya yi ishara kan nauyin da ya rataya kan kasashen biyu wato Iran da Oman na tabbatar da tsaro a matsigar ruwan Hormuz ya ce kasar Iran na iya kokarinta na ganin an tabbatar da tsaro a ruwan Oman da Tekun Fasha da mashigar ruwan Hormuz ta yadda za su kasasnce wurare masu tsaro ga jiragen ruwan dakon man na kasa da kasa.

Shugaban Rouhani ya kara da cewa sake gina kasar siriya da komawar 'yan gudun hijra kasarsu, da kuma kokari na dakatar da kisan gillar da ake yiwa al'ummar kasar Yemen na daga cikin mahiman batutuwan da ya kamata kasashen yankin su sanya a gaba, sannan kuma ya kara da cewa wuce gona da irin sahayuna da kuma kisan gillar da ake yiwa al'ummar Palastinu, rusa gidajensu da kuma shirye-shirye da ake yi kan makomar Palastine masu hadari bisa shirin nan na yarjejeniyar Karni, abun damuwa da ban takaici ne.

Yayin da yake ishara kan cewa kasar Iran ba ta taba tsokanar wata kasa ba, Rouhani ya ce rikicin dake faruwa a yankin sakamako ne, na ficewar kasar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar da kasar Iran ta cimma da manyan kasashe biyar na Duniya gami da kasar Jamus.

A nasa bangare, Minisdtan harakokin wajen Oman Yusuf bn Alawi ya bayana alakar dake kasashen biyu ta amintaka ce da dan uwanci, sannan ya kara da cewa a yau yankin gabas ta tsakiya na kan hanyarsa na fita daga cikin wani rikici mai sarkakiya kuma na tabbatar da cewa tabbatar da tsaro a yankin ba tare da kasar Iran ba, abu ne da ba zai yiyu ba.

3830542

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: