IQNA

23:59 - August 01, 2019
Lambar Labari: 3483903
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa matsugunnan yahudawa za su ci gaba da kasance cikin Isra’ila.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya habarta cewa, a rangadin da Benjamin Netanyahu ya yi yau a matsugunnin yahudawa na Afrat a gabashin quds, ya bayyana cewa dukaknin matsugunnan za su ci gaba da kasance cikin Isra’ila har abada.

Ya ce babu wani daga cikin matsugunnan yhudawa da za a rusa, domin dukkanin yankunan mallakin yahudawa ne.

Yahudawa suna ci gaba da yin fatali da yarjejeniyar Oslo ta 1995, wadda ta tabbatar da yankin yamma da gabar kogin Jordan ga Falastinawa, tare da rarraba yankin zuwa A, da B, da kuma G.

3831590

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: