IQNA

Makiya Basa Iya Jurewa Kalaman Gaskiya Da Ke Kalubalantar Zalunci Da Girman Kai

23:26 - August 02, 2019
Lambar Labari: 3483906
Bangaren siyasa, dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran sun fitar da bayani, wanda a cikinsa suke yin tir da Allawadai da matakin da Amurka ta dauka na kakaba wa Zarif takunkumi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, dakarun kare juyin Musulunci na Iran sun yi tir da takunkumin da Amurka ta sanya wa ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Dr. Muhammad Jawad Zarif suna mai bayyana hakan a matsayin wani abin ban dariya kana kuma matakin da ya saba wa doka da nufin kara matsin lamba wa Iran.

Dakarun kare juyin Musulunci sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce sanya wa babban jami’in diplomasiyyar na Iran takunkumi wata alama ce da ke nuni da damuwar da Amurka take ciki dangane da irin nasarorin da Iran take samu da kuma bakar aniyarsu ga kasa da kuma al’ummar Iran.

Kafin hakan ma dai shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Rouhani ya soki wannan matsaya ta Amurkan yana mai bayyana hakan a matsayin wani abu da yayi kama da kuruciya da rashin sanin makamar aiki.

A shekaran jiya ne ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar da kakaba wa Zarif din takunkumi, lamarin da kasashe daban-daban na duniya suke ci gaba da yi masa tofin Allah tsine.

 

3831693

 

captcha