IQNA

An Hana Maniyyata Dubu 10 Shiga Makka Domin Aikin Hajji

23:44 - August 05, 2019
Lambar Labari: 3483917
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudiyya sun hana maniyyata dubu 10 shiga cikin birnin Makka domin aiki hajji saboda rashin cikakkun takardu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Sami Al-shuwairikh kakakin hukumar tsaro ta cikin gida a Saudiyya ya bayyana cewa, sun tsayar da maniyyata kimanin dubu 10 da ba su cika sharuddan gudanar da aikin hajji ba.

Jami’in ya ce akwai tsari na musamman da ake yin amfani da shi ga  dukkanin ‘yan kasar da suke son gudanar da aikin hajji, inda sukan samu takardun izini, domin kaucewa haifar da cunkoso a yayin aikin hajji.

Ya ce mutane 288 ‘yan kasashen waje ne mazauna kasar ta Saudiyya, yayin da sauarn fiyen da dubu tara kuwa ‘yan kasar ta Saudiyya ne, wadanda ba su da takardun samun izinin gudanar da aikin hajji na wannan shekara.

Wannan tsari dai ya tanadi kayyade adadin ‘yan kasashen waje daga dukkanin kasashen duniya da suke gudanar da aikin hajji a kowace shekara, kamar yadda kuma ya kayyade adadin ‘yan kasar ko mazauna kasar da za su iya gudanar da aikin hajji a cikin shekara.

3832557

 

 

captcha