IQNA

23:01 - August 11, 2019
Lambar Labari: 3483937
Bangaren kasa da kasa, ‘yan sandan kasar Norway sun harin da aka kai masallacin Nur hari ne na ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto daga shafin Al’ayi cewa, jami’an ‘yan sanda kasar Norway, sun bayyana cewa harin da wani mutum ya kai a masalalcin Nura  cikin birnin Oslo fadar mulkin kasar, aiki ne ta’addanci.

Roney Scold babban jami’in ‘yan sanda a kasar Norway ya bayyana, cewa, masu tsatsauran ra’ayin kin jinin baki a kasar Norway ne suka kai hari a  kan masalalcin Nur, wanda wuri ne na ibadar musulmi.

Ya ce ko alama rudunar ‘yan sanda ta kasar ba za ta yi saku-saku da ayyuka irin wadannan ba, domin kuwa ayyuka ne na ta’addanci bisa dokar kasar.

A jiya ne wani mutum ya shiga masalalcin Nur da ke Osloa  kasar ta Norway ya bude wutar bindiga, amma bai kashe kowa ba.

3834314

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: