IQNA

23:41 - August 16, 2019
2
Lambar Labari: 3483954
Bangaren kasa da kasa, sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky ya koma Najeriya bayan kasa samun daidaito kan batun maganinsa a India.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya nakalto daga shafin al’ahad cewa, jagoran harkar musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun isa Najeriya bayan da su ka baro India da su ka je neman magani.

Rahotannin da suke fitowa daga Najeriya sun ambaci cewa; Bayan saukarsu a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, jami’an tsaro na farin kaya DSS sun yi awon gaba da su zuwa inda ake tsare da su gabanin tafiyarsu.

Shugaban Harkar musuluncin ta Najeriya, ya isa Najeriya ne a jirgin Ethiopia wanda ya sauka da misalin karfe sha biyu na rana.

A lokacin da yake kasar ta India, shehun malamin ya yi koken cewa ana tsakura masa ta hanyar tsaro mai tsanani da kuma rashin samun likitocin da ya aminta da su.

A ranar Litinin din da ta wuce ne dai Sheikh Ibrahim Zakzaky ya isa kasar India bisa hutun neman magani da wata Kotu a jahar Kaduna ta ba shi.

3835216

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
ALLA YABAMU ZAMAN LAFIYA
Asharaf Usman
0
0
Ni Dan Izalane Amma Ina Goyan Bayan A Saki Zakzaky Bana Tinanin Abinda Akaimai Ya Cancanta.
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: