IQNA

23:44 - August 16, 2019
Lambar Labari: 3483955
Bangaren kasa da kasa, mai bayar da shawara ga babban mufti na Masar ya bayar da shawarwari kan hanyar hardar kur’ani mafi sauki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na sadal balad ya baya da rahoton cewa, Majdi Ashur mai bayar da shawara ga babban mufti na Masar ya bayar da shawarwari kan hanyar hardar kur’ani mafi sauki ga masu masu son harda.

Ya ce ga masu shekaru suna iya hardace kur’ani cikin sauki ta hanyar hardace ayoyin da basu wuce layuka 5  ba a kowace rana, ya ce yin hakan zai taimaka ma mutun cikin sauki ya tuna abin da ya hardace.

Dangane da mahaifa kuma ya bayyana cewa, yan akyau iyaye su mayar da hankali waje tarbiyar yaransu ta hanyar shagatar da su da kur’ani, musamman ma yadda a halin yanzu tarbiya ke saurin bacewa saboda hanyoyi na yanar gizo.

Ya kara da cewa wannan hanya an jarraba ta kumaan samu dacewa matuka.

 

3835237

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: