IQNA

23:59 - August 23, 2019
Lambar Labari: 3483980
Bangaren kasa da kasa, kawancen Amurka da ke da’awar yaki da Daesh ya mayar da martani kan Hashd Sha’abi dangane da hare-haren da aka kai musu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kawancen Amurka da ke da’awar yaki da Daesh ya fitar kan bayanin Hashd Sha’abi dangane da hare-haren da aka kai musu ya bayyana cewa, manufar wannan kawance ita ce taimaka masojojin raki wajen yaki da Daesh.

Ya kara da cewa, gwamnatin Iraki ce da kanta ta bayar da dama ga wanann kawance kan ya gudanar da ayyukansa  acikin Iraki.

Wannan bayani na zuwa ne bayan gaegadin da dakarun Hashd Sha’abi suka yi wa Amurka ne, kan zargin cewa it ace ta taimaka ma Isra’ila wajen kai hare-hare a kan wasu wuraren ajiye makamai na dakarun Hashd Sh’abi a cikin Iraki, inda suka ce sun baiwa Amurka gargadi na karshe.

 

3836765

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: