IQNA

23:52 - September 02, 2019
Lambar Labari: 3484011
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar kur’ani a New Oakland a jihar Massachusetts Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin Metro Daily West News ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da gasar kur’ani a New Oakland a jihar Massachusetts Amurka tare da halartar makaranta matasa 150.

Cibiyar Boston da ke kula da harkokin addinin muslunci ita ce ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan gasa.

Tun kafin wannan lokacin dai an gudanar da zama na share fagen gasar, tare da fitar da dukkanin wadannan za su halarci gasar.

Bangarorin gasar dai sun hada da tilawa da kuma harda a dukkanin bangarori, kama dag ahardar dukaknin kur’ani da kuma rabi da rubu’i.

Babbar manufar gasar dai ita ce kara karfafa gwiwar matasa musulmia  kasar wajen mayar da hankali ga lamarin kur’ani mai tsarki.

رقابت 150 نفر در مسابقات قرآن ماساچوست

رقابت 150 نفر در مسابقات قرآن ماساچوست

رقابت 150 نفر در مسابقات قرآن ماساچوست

3839317

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: