IQNA

23:56 - September 02, 2019
Lambar Labari: 3484012
Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana cewa, babu wata alaka tsakanin addinin muslucni da kuma ayyukan ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana furucin jami’an India kan cewam matakin da suka dauka kan Kashmir yana a matsayin yaki da ta’addanci ne da cewa, wannan magana ce ta wofi.

Ya ce babu yadda hankali zai yadda da cewa, za a iya hukunta al’umma guda baki dayanta da aikin mutum guda, a kan haka ya ce wannan matakin an India a kan musulmin Kashmir yana da alaka da siyasa da kuam nuna wariya ta akida ga musulmi.

A kan haka firayi ministan kasar ta Pakistan ya ce nauyi ne da ya rataya kan al’ummomin duniya baki daya da su kare al’ummar Kashmir daga neman kawar da su da ake yi daga samuwa.

A ranar 5 ga watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin kasar Indiya ta soke doka mai lamba 370 da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar, wadda ta baiwa yankin Kashmir kwarkwaryan cin gishin kai.

 

 

 

3839064

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، pakistan ، India ، Kashmir
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: