IQNA

23:51 - September 03, 2019
Lambar Labari: 3484013
Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren Hizbullah ya bayyana martanin kungiyar a kan Isra’ila a matsayin wani sabon shafi na kare kasar Lebanon daga shisshigin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyd Hassan Nasrullah, ya bayyana martanin kungiyar a kan Isra’ila a ranar 1 ga wannan wata na Yuli da cewa, hakan na a matsayin bude wani sabon shafi ne a bangaren daukar sabbin matakai na kare kasar Lebanon daga shisshigin Isra’ila.

Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hakan ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa da ya kan gabatar a cikin kwanaki 10 na Ashura, a babban dakin taro na Husainiyar Sayyid Shuhada da ke kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

A cikin jawabin nasa, Sayyid Nasrullah ya bayyana martanin kungiyar a kan shishigin Isra’ila a kan Lebanon da cewa ya gudana acikin nasara kamar yadda aka shirya shi, kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa, bisa masaniya ne dakarun Hizbullah suka kaddamar da harin a da rana tsaka maimakon da dare.

Haka nan kuma ya bayyana wannan mataki da cewa yana a matsayin bude sabon babi ne na shiga kafar wando daya da Isra’ila a kan duk wani matakin tsokana da za ta sake dauka a kan kasar Lebanon a nan gaba, inda ya ce hatta jiragen yaki marassa matuki da Isra’ila take turawa a cikin Lebanon, Hizbullah za ta fara kakkabo su ba tare da wani shayi ba.

Dangane da sako na siyasa da ke tattare da abin da ya faru kuwa, Sayyid Nasrullah bayyana cewa, duk wata haiba da tinkaho na Isra’ila ya kawo karshe, domin kuwa kungiyar Hizbullah ta tabbatar wa duniya musamman kasashen da suke tsoron Isra’ila, da cewa ba ta kai yadda suke tsammani ba, domin kuwa bayan harin Hizbullah, dukkanin sojojin Isra’ila da suke kusa da iyakokin Lebanon, sun tsere zuwa tsawon kilomita 7.5 daga kan iyakar Lebanon saboda tsananin tsoro da razana, kamar yadda kuma dukkanin jiragen yaki marassa matuki da Isra’ila ta turo cikin Lebanon ba su iya yin nasarar aiwatar da aikinsu ba.

Dangane matsayar da gwamnatin Lebanon ta daukia kan wannan batu kuwa, Sayyid Hassan Nasrullah ya jinjinawa dukkanin jami’an gwamnatin Lebanon kan matsayar da suka dauka ta nuna goyon bayansu ga wannan martani na Hizbullah a kan Isra’ila, kama daga shugaban kasa da sauran manayan jami’ai, da kuma rundunar sojin kasar ta Lebanon, wadda take amatsayin babbar mai karfafa gwiwa Hizbullah, kuam take a kan iyakoki tana dakon makiya.

Da dama daga cikin masana harkokin soji na Isra’ila da suka bayyana ra’ayoyinsu kana bin da ya faru abin kunya ne ga rundunar sojin Isra’ila, kamr yadda yake abin kunya ga Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda shi ne ya bayar da umarnin yin haka, wanda kuma hakan yana da nasa babban tasirin ga makomarsa a fagen siyasar Isra’ila, domin kuwa ya bayar da umarnin kaiwa Hizbullah hari ne domin ya samu kuri’aazabe, ta hanyar tabbatarwa yahudawan Isra’ila cewa shi jarumi ne, amma kuma bai yi nasara ba, maimakon haka ma ya jawo wa Isra’ila abin kunya, domin mayakn Hizbullah sun fatattakin sojojin Isra’ila daga kan iyakokin Lebanon.

 

3839566

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: