IQNA

23:25 - September 05, 2019
Lambar Labari: 3484020
Bangaren kasa da kasa, A karon farko cikin tarihin Sudan an zabi Mace a matsayin ministar harakokin wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Rusia Today bayar da rahoton cewa, Firaministan rikon kwaryar kasar Abdullah Hamdouk na gabatar da sunayen ministocin gwamnatinsa 14 a jiya Laraba, daga cikinsu har da sunan Asama'u Abdullahi wacce aka bata mukamin ministar harakokin wajen kasar.

Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kasar Sudan da wata Mace za ta rike ma'aikatar harakokin wajen kasar.

Dangane da wannan batu, yayin da yake gabatar da taron manema labarai da ministan harakokin wajen kasar Jamus Heiko Maas, Piraministan kasar Sudan Abdullah Hamdouk ya tabbatar da cewa hakkin Mata ne a dama da su cikin harakokin siyasar kasar ta Sudan.

Majalisar Zartarwar ta rikon kwaryar ta Sudan na kunshe ne da Mutane 11, biyar daga bangaren Majalisar mulkin kasar, da kuma biyar daga bangaren gamayyar kungoyin neman 'yanci da sauyi wadanda suka yi fafutukar tunbuke gwamnatin shugaba Al-Bashir, sai kuma Mutum guda daga cikin bangaren kungiyoyin farar hula na kasar.

3839930

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: