IQNA

23:53 - September 08, 2019
Lambar Labari: 3484029
Bangaren kasa da kasa, fitacciyar mawaiyar Ireland da ta muslunta ta bayyana cewa daga lokacin da ta karanta kur’ani sai ta fahimc cewa ita musulma ce.

Kamfanin dillacin labaran iqna ya nakalto daga mujallar Mirror cewa, Sinead O'connor fitacciyar mawaiyar Ireland wadda ta muslunta a shekarar da ta gabata ta bayyana cewa; daga lokacin da ta karanta kur’ani sai ta fahimc cewa ita d ma can musulma ce amma ba ta fahimta ba.

Ta ce tana alfahari da kasancewarta musulma, domin kuwa ta fahimci cewa muslunci shi ne addini da ya dace da dukkanin ‘yan adam a  hankalce.

Ta kara da cewa, lokacin da ta karanta kur’ani zai ta ji da ita musulma ce, amma saboda wani yanayi ne ba iya gano haka ba tsawon rayuwarta, amma karanta kur’ani ya tunatar da ita ta gane addininta na asai.

Wannan shararriyar mawakiya ta musluncta ne a shekarar da ta gabata, kuma labarin musuluntarta ya dauki hankulan kafofin yada labarai na duniya.

 

 

 

3840847

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulma ، Ireland
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: