IQNA

23:20 - September 13, 2019
1
Lambar Labari: 3484047
Bangaren kasa da kasa, kasashen Jamus, Birtaniya, Faransa, Italiya da Spain sun yi watsi da shirin  Netanyahu.

Kamfanin dillancin labara iqna, jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, wadannan kasashe biyar sun fitar da bayanin nasu ne na hadin gwiwa, domin nuna rashin amincewa da furucin da Netanyahu ya yi, kan cewa idan ya lashe zabe zai hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan da sauran yankunan Isra’ila.

Bayanin ya ce wannan mataki da Netanyahu yake barazanar dauka, zai karo da dukkanin ka’idoji da kuma dokoki na kasa da kasa, a kan haka ba za su taba amincewa da wannan yunkuri ba.

A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana wanna mataki da Netanyahu ke shirin dauka da cewa yana da karya zuciya, kuma ya yi hannun riga da dukkanin dokokin duniya.

A cikin makon da ya gabata ne Firayi minister Isra’ila Bejamin Netanyahu ya fadi a wajen yakin neman zabe cewa, idan ya lashe zaben da za a gudanar a cikin wannan mako, zai hade yankunan Falastinawa na gabar yamma da Kogin Jordan da Isra’ila.

 

3841772

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Israel's laanniyar ka
sace
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: