IQNA

23:48 - September 14, 2019
Lambar Labari: 3484051
Kungiyar Amnesty ta bukaci a hukunta wadanda suke  da hannu a kisan da aka yi masu zanga-zanga a Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kungiyar kasa da kasa ta kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bukaci a hukunta dukkanin wadanda suke  da hannu a kisan da aka yi masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Albashir.

Wannan kira yan zwa nea ziyarar da babban daraktan kungiyar ya kai kasar Sudan ne, wanda kuma shi ne karon farko da ya ziyarci kasar, inda ya jinjina wa al’ummar Sudan kan yadda suka mike suka kwaci ‘yancinsu da kansu daga abin da ya kira mulkin kama karya.

Tun a cikin watan Disan 2018 ne aka fara bore a kasar Sudan, domin nuna rashin amincewa da yanayin da kasar ta fada na talauci da matsaloli na tattalin arziki, inda jama’a suka fito kwansu da karkwatarsu wajen neman Albashir a sauka daga kan karagar shugabancin kasar, bayan da tura ta kai bango.

Daga karshe dai boren jama’a ya tilasta sojoji suka yi wa Umar Abashir juyin mulki wanda ya kawo karshen mulkinsa wanda ya kwashe shekaru kimanin talatin a kansa.

3841978

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: