IQNA

23:42 - September 16, 2019
Lambar Labari: 3484057
Bangaren kasa da kasa, Firayi ministan Isra’ila ya ce bayan kammala zaben Kneset za a gabatar da shirin yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palestine cewa, a cikin wani jawabinsa a yau, Netanyahu ya bayyana cewa; bayan kammala zaben Knesset da ‘yan kwanaki Amurka za ta gabatar da shirinta na yarjejeniyar karni.

Netanyahu ya ce ya nada shugaban ofishinsa domin ya jagoranci shirin mamaye yankunan falastinawa na Agwar da har zuwa dead sea.

Ya kara da cewa, mayar da yankunan gabar yamma da kogin Jordan da kuma Agwar na da matukar muhimmanci ga makomar tsaron Isra’ila, a kan haka wannan zai zama daya daga cikin bangarori na yarjejeniyar karni.

3842499

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، bangarori ، zama ، agwar ، Netanyahu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: