IQNA

23:39 - September 20, 2019
Lambar Labari: 3484069
Bangaren kasa da kasa, cibiyar azahar ta mika sakon ta’aziyya dangane da rasuwar daliban kur’ani sakamakon wata gobara a Liberia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sakon da ta aike a jiya, cibiyar azahar ta mika sakon ta’aziyya dangane da rasuwar daliban kur’ani sakamakon wata gobara a Liberia tare da rokon Allah yayi musu rahama.

A daren Talata da ta gabata ce dai wata gobara ta tashia  cikin wata makarantar kur’ani a birnin manrovia fadar mulkin kasar Liberia, inda yara daliban kur’ani 27 tare da malamansu guda biyu suka rasa rayukansu.

Jami’an ‘yan sanda sun ce ba a san dalilin tashin gobarar ba, amma har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabinta.

 

3843255

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: