IQNA

22:53 - September 24, 2019
Lambar Labari: 3484084
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Amurka sun gudanar da jerin gwano domin jaddada wajabcin hadin kan al'ummar musulmi a New York.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Aljazeera cewa, a jiya dubban musulmi sun yi wani jerin gwano a birnin new na Amurka, domin jaddada hadin kan msuulmin kasar.

Rahoton ya ce kimanin musulmi 3000 ne suka shiga cikin wannan jerin gwano, inda suke rera taken hadin kai da kuma tabbatar da samuwarsu a matsayin 'yan kasa da suke da cikakken 'yancin yin addininsu.

Adams Fufana dan asalin kasar Ivory Coast wanda yake yanzua  Amurka, ya ce suna gudanar da irin wannan jerin gwano duk shekara, kuma hakan yana kara karfafa gwiwar musulmin Amurka domin jin cewa suna da 'yanci a kasar.

3844391

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، musulmi ، jerin gwano
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: