IQNA

23:53 - October 01, 2019
Lambar Labari: 3484106
Bangaren kasa da kasa, an kafa kwamitin bincike na mutane 24 dangane da keta alfarmar kur’ani mai tsarki a jihar Zamfara Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Daily Trust ta Najeriya cewa; Bello Muhammad Matawalle gwamnan jihar Zamafara ya bayyana cewa, ba za su daga kafa ga duk wanda yake ta alfarmar kur’ani mai tsarki a jiharsu ba.

Matawale yce an kafa kwamitin ne domin bin kadun lamarin tare da gno masu hannu a  cikin lamarin, ya ce za a hukunta duk wanda aka samua  cikin wanann lamari na keta alfarmar kur’ani ba tare da la’akari da matsayinsa ba ko shi wane ne.

A cikin makon da ya gabata ne dai aka keta alfarmar kur’ania  wata makaranta a garin Gusau fadar mulkin jihar Zamafara, lamarin da ya daga hankulan al’ummar jihar.

 

3846328

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، Zamfara ، Matawalle
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: